Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Ƙarin farashin mai da lantarki: NLC ta ba gwamnati wa’adin sati biyu

Ƙarin farashin mai da lantarki: NLC ta ba gwamnati wa’adin sati biyu

110
0

A ranar Larabar nan ne ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya NLC, ta ba gwamnatin tarayya wa’adin sati biyu da ta janye matakinta na ƙara farashin mai da hasken lantarki.

NLC da sauran ƙungiyoyi ƙawayenta, sun nace cewa matuƙar gwamnatin bata saurare su ba, za su tafi yajin aiki na sai baba ta gani tare da gangamin Zanga-zanga a faɗin ƙasar daga ranar 28 ga watan Satumba.

Shugaban ƙungiyar Ayuba Wabba, wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwar bayan taron da kwamitin ayyukan ƙungiyar ya gudanar a Abuja, ya ce ƙarin farashin, ya sanya ƙarin albashi mafi ƙaranci da aka yi ya zama marar amfani saboda hauhawar farashi a ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply