An samu rahoton mutum biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar Covid-19 a jihar Kogi.
Waɗannan dai sune na farko da aka tabbatar da sun kamu da cutar a jihar ta Kogi wadda ta daɗe ba a samu ɓullar cutar a jihar ba.
Hukumar NCDC ce ta sanar da hakan a shafin ta na Twitter lokacin da take sanar da mutum 389 da suka kamu da cutar a ranar Laraba.
Wannan dai shi ne adadi mafi yawa da Nijeriya ta samu tun bayan ɓarkewar cutar a ƙasar, inda yawan waɗanda suka kamu da cutar ya kai 8,733 daga ciki an sallami 2,501 sai kuma 254 sun mutu.
