Home Labarai Ƙasashen OPEC+ za su rage yawan man da suke haƙowa

Ƙasashen OPEC+ za su rage yawan man da suke haƙowa

127
0

Ƙungiyar ƙasashe masu arziƙin man fetur OPEC da sauran ƙasashen da ba su cikin ƙungiyar ƙarƙashin jagoranci Rasha sun amince da rage yawan man da suke haƙowa zuwa ganga miliyan 9 da dubu 700 a kullum.

Wannan ya nuna an samu ƙarin ragin ganga dubu 300 daga ganga miliyan 10 da ƙasashen suka zartar za a iya haƙowa kullum, a taron da suka gudanar ta intanet a ranar Alhamis.

Taron na gaggawa na makon jiya dai ƙasar Saudiyya ce ta shirya shi domin samar da matsaya kan man da ake haƙowa don daidaita kasuwar sa da kuma dakatar da faɗuwar farashin sa.

Saidai aiwatar da wannan mataki ya ci karo da cikas bayan da ƙasar Mexico 🇲🇽 wadda ba ta cikin ƙungiyar OPEC ta ce ba za ta rage man da take haƙowa a rana da ganga dubu 400 ba.

Shugaban Mexico 🇲🇽 Andres Obrador ya bada sanarwar cewa kamfanin haƙar man ƙasar zai iya rage ganga dubu 100 ne kacal a rana.

A kan haka ne aka sake kiran wani taron gaggawa a jiya Lahadi domin tausar Mexico 🇲🇽 ta sauya ra’ayin ta a kan batun.

A ƙarshen taron ne wanda wakilan Mexico 🇲🇽, Amirka 🇺🇸, da Canada 🍁 duk sun halarta aka samar da matsayar rage ganga miliyan 9 da dubu 700 a rana.

A ƙarƙashin wannan tsari dai, akwai yiwuwar Nijeriya 🇳🇬 za ta rage adadin man da take haƙowa da ganga 417,000 a ko wace rana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply