Home Labarai Ƙungiyoyin na bada tallafin karatu a jihar Kebbi

Ƙungiyoyin na bada tallafin karatu a jihar Kebbi

70
0

Wata gamayyar kungiyoyi masu fafutukar ci gaban Ilimi a jihar Kebbi sun fara aikin raba kayan karatu ga dalibai musamman a makarantun boko na ƴaƴan marassa galihu a fadin jihar ta Kebbi.

Aikin raba kayan da ya kunshi litattafai, kayan makaranta, Hijabai ga dalibai mata, da kuma takunkumin rufe fuska da kuma man wanke hannu.

Kungiyoyin dai da suka haɗa da Argungu Educational Aids da kuma Khadimiyya suna wannan aikin ne don saukakawa yaran marassa galihu a harkar karatu, domin su zamo dai-dai da kowa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply