Gwamna Alhaji Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi aiki da ƴan kwangila da ma Injiniyoyi ƴan asalin jihar domin a kara6 inganta tattalin arziƙin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da wakilan majalisar da ke kula da ayyukan Injiniyoyi ta ƙasa a garin Gombe.
Ya kuma ce gwamnatin jihar na da manufar ƙara inganta ayyukanta ta hanyar haɗa kai da Injiniyoyi da ƴan kwagilar jihar cikin ayyukansu na raya jihar domin amfanuwar al’umma baki ɗaya.
