Home Labarai Ƴan bindiga sun kashe DPO sun yi garkuwa da mata biyu a...

Ƴan bindiga sun kashe DPO sun yi garkuwa da mata biyu a Sokoto

201
0

Ƴan bindiga sun kashe baturen ƴan sandan ofishin Gidan Madi da ke ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Ƴan bindigar sun kuma kashi wani jami’in ƴan sandan sannan suka sace matan wani sanannen ɗan kasuwa a yankin.

Rahotanni sun ce an kashe ƴan sandan ne a lokacin da suke ƙoƙarin ceto matan biyu da aka sace da misalin ƙarfe ɗaya na daren Alhamis, yayin da wasu kuma suka ce ƴan bindigar sun fara kai hari a ofishin ƴan sandan ne suka kashe su, sannan suka je suka sace matan.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Sokoto ASP Muhammad Sadiq ya tabbatar da faruwar al’amarin, saidai ya yi kira da a guji yaɗa wasu bayanai har sai ƴan sanda sun gama bincikensu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply