Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargadin cewa kungiyar Boko Haram na iya fakewa da cutar Covid-19, ta kaddamar da hare-hare a wasu sassan Nijeriya.
A cikin sabuwar sanarwar da ta fitar kan bayanan barazanar tsaro da shawarwari, sashen tsaro na majalisar ya ce za a yiwa hana aukuwar hare-haren idan har an dauki matakan da suka dace.
Sashen tsaro na majalisar dinkin duniyar, ya ce bayanan sirri sun nuna cewa za a iya kitsa hare-haren ne a yankunan da kungiyar ke aikin ta, musamman kan muhimman gine-ginen gwamnati.
Ta kara da cewa, baya ga gurgunta kokarin gwamnati a kan tsaro, kungiyar za ta yi kokarin yin wasa da hankalin jami’an tsaro, ga aikin da suke a Arewa aso Gabas.
Domin dakile wannan matsala, majalisar dinkin duniyar ta bada shawarar a yi bitar tsarin kyautata matakan tsaro tare da aiwatar da sabbin tsare-tsaren.
