Home Labarai Ƴan Boko Haram sun harbo jirgin Nijar a Borno

Ƴan Boko Haram sun harbo jirgin Nijar a Borno

267
0

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun harbo wani jirgin sama mai saukar angulu na ƙasar Nijar ɗauke da wasu fasinjoji da ba a tantance ko su waye ba a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kusa da garin Banki da misalin karfe 10 na safiyar yau Talata, mutum biyar da ke cikin jirgin sun mutu a hatsarin nan take.

Wata majiya da ta kai agajin gaggawa tare da Sojoji ta tabbatar jirgin na ƙasar Nijar ne kuma alamu sun nuna kabo jirgin aka yi.

Ya zuwa lakocin haɗa wannan rahoto rundinar Soji bata ce komai ba akan afkuwar lamarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply