Home Labarai Ƴan Boko Haram sun kashe jami’an tsaro uku a Borno

Ƴan Boko Haram sun kashe jami’an tsaro uku a Borno

44
0

Wasu ƴanta’adda da ake zargi ’yan Boko Haram ne sun kai hari tare da kashe wasu mutum uku a shingen binciken ababen hawa da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Gubio a ranar Lahadi.

Wani babban jami’in kungiyar sa-kai, Bakura Aliyu ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawarsa da jaridar Daily Trust.

Majiyar DCL Hausa ta bayyana cewa mayakan na Boko Haram sun kai farmaki shingen binciken da ke tsakanin yankin Chabol da Magumeri da misalin karfe 12:30 na rana, inda suka kashe wasu jami’an ’yansanda biyu da wani dan kungiyar sa-kai yayin da suka riƙa harbin kan mai uwa da wabi.

Wata majiyar ta shaida cewa maharan sun kuma kone wata motar sintiri yayin da suka arce da guda daya bayan sun tarwatsa jami’an tsaron da ke sansanin binciken.

Majiyar ta ce, “lamarin ya faru a ranar da Sabbin hafsoshin tsaro suka kai ziyara a Maiduguri don ganin an shawo kan matsalar tsaro a yankin”.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply