Home Kasashen Ketare Ƴan Boko Haram sun kashe mutane 14 a Kamaru

Ƴan Boko Haram sun kashe mutane 14 a Kamaru

96
0

Mayakan Boko Haram sun kashe mutum 14 a wane hari da suka kai daren Juma’ar nan a garin Mozogo da ke Arewacin Kamaru.

A baya-bayan nan dai, kungiyar na kai hare-hare a yankin duk kuwa da ikirarin da gwamnati ta yi na cewa ta yi nasara a kanta.

A cewar shugaban garin na Mozogo, Boukar Medjewe mazauna yankunan na guduwa cikin daji da zaran sun samu labarin maharani na tunkarar garinsu.

Wani dan kunar bakin wake ne dai, da ya shiga cikin masu guduwar, ya tada bom da ya yi silar mutuwar mutum 11 nan take kafin ‘yanbindiga su kashe wasu karin hudu.

Ya ce jami’an tsaro sun yi saurin zuwa inda abun ya faru, saidai ba su yi harbi ba, saboda ‘yanta’addan sun cakudu da farar hula.

Da yawa daga cikin jama’ar kasar na sanya alamar tambaya dai ga wannan ikirari na gwamnati da ke cewa ta kusa kawo karshen kungiyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply