Home Labarai Ƴan Boko Haram sun kashe sojoji 10 a Borno

Ƴan Boko Haram sun kashe sojoji 10 a Borno

201
0

Wasu da ake zargin ‘yan tada kayar baya ne, sun kashe sojojin Nijeriya goma a jihar Borno, kamar yadda wata majiya ta tabbatar.

A cewar majiyar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya faru ne a yankin Alagarno da ke karamar hukumar Daboa, saidai hukumomi ba su yi Karin bayani kan batun ba.

Majiyar ya ce mayakan ISWAP sun farwa sojojin da ke kusa da hanyar Alagarno, inda suka kashe sojojin goma tare da sace daya.

A lokacin harin, ‘yan ta’addan sun sace tankokin yaki hudu, da kayan yakin rundunar sojojin kamar yadda majiyar, ya shaida wa Daily Trust.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply