Home Labarai Ƴan gidan yari 36 sun kammala karatun digiri

Ƴan gidan yari 36 sun kammala karatun digiri

37
0

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan gidan yari 18 sun kammala karatun jami’a a jami’ar karatu daga gida (NOUN) a fannoni daban daban.

A cikin sakon taya murna da jami’in rikon kwarya na hukumar gidan gyaran hali John Mrabure ya fitar, ya bukacesu da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen habbaka rayuwarsu ta nan gaba.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar gidan yari Francis Enobore a cikin sanarwar ya bayyana cewa shugaban ya kirayi ƴan gidan yarin su guji sake fadawa cikin dabi’u marasa kyau don gudun gurbata sabuwar rayuwar da suka dauko, su zama wakilai na gari ga hukumar tasu da jami’ar baki daya.

A cikin gidajen yarin da suka yaye daliban sun hada da na Awka, Enugu, Kuje, Fatakwal da Kirikiri da ke jihar Lagos.

Majiyar DCL Hausa ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu akwai ƴan gidan yari 3,000 da ke karatu afannoni daban daban na jami’ar yayin da 50 ke karatun NCE a kwalejin ilimi dake jihar Ogun.

“Tun bayan hadaka tsakanin jami’ar karatu daga gida da hukumar gyaran hali an yaye dalibai 36 a kokarin ganin an inganta rayuwarsu tare da kawar da ta’addanci a kasar nan” Inji sanarwar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply