Home Labarai Ƴan kwana-kwana sun ceto dukiya da ta kai ₦1trn daga gobara

Ƴan kwana-kwana sun ceto dukiya da ta kai ₦1trn daga gobara

103
0

Ministan cikin gida Rauf Argbesola ya ce gwamnatin tarayya na aiki tukuru wajen inganta ayyukan jami’an kashe gobara.

Ministan ya bayyana cewa an samu tashin gobara sama da 2,000 a cikin shekarar 2020, inda hukumar kashe gobara ta tarayya ta yi nasarar ceto rayukan mutane 724 da dukiyoyin da suka kai darajar Naira Tiriliyan daya daga gobara.

Aregbesola ya bayyana haka ne a birnin Akure, lokacin da yake kaddamar da wata motocin kashe gobara na miliyoyin Naira, da gwamnatin tarayya ta ba jihar Ondo a ranar Litinin, yana mai cewa ya zo jihar ne don wayar da kan jama’a, a kan hadarin gobara.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya ce gwamnatinsa na kokarin samar da tashoshin kashe gobara da inganta su a fadin jihar, tare da karfafa jami’an hukumar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply