Home Labarai Ƴan majalisa na yinƙurin tsige gwamna Bagudu

Ƴan majalisa na yinƙurin tsige gwamna Bagudu

829
1

A daidai lokacin gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ke jagorantar ƙoƙarin daidaita rikicin APC a jihar Edo, ƴan majalisar dokokin jihar sa sun fara yinƙurin tsige shi.

Binciken da Jaridar Guardian ta yi, ya nuna cewa an shiga takun saƙa tsakanin gwamnan da ƴan majalisar biyo bayan rashin aiwatar da wasu ƙudurori da Majalisar ta aike masa.

Rahotanni sun nuna cewa a lokacin wani taron gaggawa ƴan majalisar sun aiwatar da wasu ƙudurori 3 da suka buƙaci gwamnan ya aiwatar da su cikin gaggawa.

Sun kuma yi gargaɗin matuƙar ba a ɗauki wannan mataki ba to za su yi duk abun da ya dace don kare ƴancin da kundin tsarin mulki ya ba su.

Saidai kuma kusan bayan wata guda da ƴan majalisar suka yi wannan gargaɗi gwamnan ya yi biris da su, wanda ya sanya suka fara shirin tsige shi.

Da yake tabbatar da hakan, wani ɗan majalisa da ya buƙaci a sakaya sunan sa ya tabbatar da cewa ƴan majalisar sun duƙufa kan batun tsige gwamnan kan rashin aiwatar da ƙudurorin.

Ya ƙara da cewa dole ne su yi abun da zai tabbatar su ba ƴan amshin shatan gwamnan ba ne.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply