Home Labarai Ƴan Nijeriya miliyan 15 ke tu’ammali da miyagun ƙwayoyi – NDLEA

Ƴan Nijeriya miliyan 15 ke tu’ammali da miyagun ƙwayoyi – NDLEA

61
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta alaƙanta yawan aikata laifuka da ake samu a Nijeriya da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi tana mai cewa kimanin ƴan Nijeriya miliyan 15 ne ke shan miyagun ƙwayoyin.

Sabon shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya sanar da haka a ranar Litinin a Birnin Fatakwal, lokacin ziyararsa ta farko ga sauran hukumomi da masu ruwa da tsaki a jihar Rivers.

A cewarsa, miyagun ƙwayoyi na neman illata ƙasar, ta yadda yake janyo aikata mafi yawan laifukan da ake fama da aikata su a Nijeriya.

Ya ce dukkan laifukan da suka shafi fashi da makami, satar mutane, ƴanbindiga, ƴanta’adda, tada ƙayar baya, fyaɗe da sauransu, masu tu’ammali da miyagun ƙwayoyi ne ke aikata su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply