Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Ƴan Nijeriya na kashe sama da ₦22tn kan sayen abinci

Ƴan Nijeriya na kashe sama da ₦22tn kan sayen abinci

242
0

Yawan kudin da Nijeriya ke kashewa kan abinci ya karu zuwa Naira Tiriliyan 22.78 a shekarar 2019, sama da Naira Tiriliyan 12.77 da aka samu a shekarar 2010, lokaci na karshe da aka gudanar da binciken.

Wani rahoto da hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ta fitar jiya Lahadi ya nuna cewa adadin yawan kudin da gidaje a Nijeriya ke kashewa kan abinci da sauran kayan amfani a shekarar 2019 ya kai Naira Tiriliyan 40.21 kari daga Naira tiriliyan 21.62 a shekarar 2018.

Rahoton ya kuma nuna cewa sayen abinci shi ne ya tafi da kashi 56.65% na kudaden da ko wane gida ke kashewa a shekarar, sai kuma sauran hidimomin gida da suka dauki kashi 43.35% na yawan kudin da gidaje suka kashe a shekarar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply