Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Ƴan Nijeriya na kokawa da tashin farashin gas na girki

Ƴan Nijeriya na kokawa da tashin farashin gas na girki

100
0

A Nijeriya ‘yan kasar na ci gaba da kokawa dangane da yadda farashin GAS na girki ya yi tashi goron zabi da kashi 20%.

Tashin farashin dai na zuwa ne sakamakon karyewar darajar Naira a kasuwannin musayar kuɗi, inda masu anfani da gas na girkin za su kara biyan kudade tsawon watanni masu zuwa a cewar wani Ibrahim mai samar da gas din a jihar Sakkwato.

A baya dai ana sayan Ton20 na gas a kan Naira miliyan ₦4.4m, amma yanzu ana sayar da shi kan Naira miliyan ₦5.3m.

‘Yan Kasuwar Gas sun ce farashin zai ci gaba da da hauhawa  matukar darajar Naira ta ci gaba yin kasa akan Dala.

Nijeriyar dai na shigo ne da gas na girki ne daga kasashen waje sakamakon rashin aikin matatun nan ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply