Home Labarai Ƴan rakiyar siyasa ba za su shiga filin jirgi ba – Sirika

Ƴan rakiyar siyasa ba za su shiga filin jirgi ba – Sirika

187
0

Ministan sufurin saman Nijeriya Hadi Sirika ya ce fasinjoji ne kaɗai za a ba dama su shiga cikin filin jirgi.

A ranar Laraba ne dai Ministan ya ce za a fara ɗaukar fasinjoji a filayen jiragen saman Abuja da Lagos a ranar 8 ga watan Yuli, sai kuma na Kano, Fatakwal, Owerri da Maiduguri da za su biyo baya a ranar 11 ga watan Yulin.

Sirika wanda ya bayyana haka a ranar Alhamis, ya ce duk wani wanda babu abun da zai yi a filin jirgi, musamman ƴan rakiya da muƙarraban ƴan siyasa ba za a bar su, su shiga ciki ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply