Rundunar Ƴan sanda ta jihar Zamfara haɗin gwiwa da rundunar sojojin Nijeriya sun kama tare da tsare mutane 251 da ke haƙar ma’adanai a jihar Zamfara.
Kwamishinan ƴan sandan Usman Umar Nagogo, wanda ya bayyana haka a ranar Asabar, ya ce ya jagoranci jami’an sa zuwa manyan wuraren haƙar ma’adanai na Kwalli da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum.
Ya ce a nan suka samu wasu ƴan China da masu taimaka masu ƴan Nijeriya kuma suka kama su, tare da tura su shelkwatar bincike dake Abuja.
Daga cikin kayan da aka samu daga wajen su, sun haɗa da injinan zuƙar ruwa 12, babur 29, sinadaran haɗa zinare da kuma ɗanyen zinare.
Kwamishinan ya ce dukkan masu laifin sun amsa laifukan su, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci da zaran an dawo da zaman kotuna.
