Home Labarai Ƴanbindiga sun kai hari gidan marayu a Abuja, sun sace mutum 10

Ƴanbindiga sun kai hari gidan marayu a Abuja, sun sace mutum 10

35
0

Wasu ƴanbindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari wani gidan marayu mai suna Rachael da ke yankin Abaji a birnin tarayya Abuja tare da sace marayu bakwai da wani mai gadin gidan.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu matan aure guda biyu da ke zaune a bayan gidan marayun.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na daren ranar Asabar lokacin da maharan suka shigo yankin dauke da muggan makamai sannan suka yi wa gidan kawanya ta babbar kofarsa.

A cewarsa, bayan samun nasarar shiga ne suka kwashe marayun guda bakwai da kuma mai gadin gidan guda daya.

Wani magidanci mai suna Mohammed Nuruddeen wanda aka harba tare da sace matarsa mai suna Rukayyat Salihu ya ce yana bacci lokacin da suka balle kofar gidan da karfin tsiya sannan suka tafi da matar tasa.

Kakakin rundunar ƴansandan babban birnin tarayya Abuja, ASP Maryam Yusuf ta tabbatar da faruwar lamarin, ko da ya ke ta ce mutum shida ne kawai aka sace yayin da daya kuma ya kubuta.

Ta kuma ce tuni rundunarsu ta baza jami’anta zuwa dazukan dake makwabtaka da yankin don ganin an kubutar da ragowar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply