Home Labarai Ƴanbindiga sun kashe basarake da ɗansa a Kaduna

Ƴanbindiga sun kashe basarake da ɗansa a Kaduna

146
0

Wasu ‘yanbindiga sun kashe hakimin Gidan Zaki da ke karkashin masarautar Atyap a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna, tare da dansa.

‘Yanbindigar wadanda aka ce sun shigo garin da misalin karfe 12 na daren ranar Litinin, sun kashe Hakimin Haruna Kuyet da dansa sannan suka harbi matarsa, wadda yanzu haka ake kula da ita a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin ga ‘yan jarida, sakataren karamar hukumar Zangon Kataf Elisha Sako, ya yi tir da harin, yana mai cewa an jibge jami’an tsaro a yankin domin daidaita al’amura da kuma binciko wadanda ake zargin.

Daily Trust ta ruwaito cewa harin na zuwa ne a daidai lokacin da masarautar ta atyap, gwamnati da sauran kungiyoyin da ba na gwamnati ba ke gudanar da taruka don samar da daidaito a tsakanin kabilun yankin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply