Wasu ƴanbindiga sun kashe wata jami’ar lafiya mai ɗauke da ciki wata 8, a hanyar Birnin Gwari-Kaduna, lokacin da suka buɗe wuta ka yi wata motar haya da ta nufi Kaduna.
An dai kashe matar ne a wani wuri da ake cewa Zankoro Unguwar Yako ranar Lahadi, lokacin da take hanyar zuwa Kaduna daga Birnin Gwari.
Ɗan uwan matar da aka bayyana da Aisha Yusuf, Aliyu Mahmud ya tabbatar da hakan ta wayar tarho ga Daily Trust.
Da aka tuntuɓe shi, Kakakin rundunar ƴansandan jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige, ya yi alƙawarin kiran baturen ƴansandan yankin domin jin ƙarin bayani kafin ya ce wani abu.
