Aƙalla mutane 11 ne aka kashe a wani hari da wasu ƴanbindiga suka kai a ƙauyen Albasu da ke Sabon Birni, cikin ƙaramar hukumar Igabi, ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce ƴanbindigar sun yi dirar mikiya a garin, suka riƙa harbin kan mai uwa da wabi, da misalin ƙarfe 1pm na ranar Litinin, inda suka kashe mutane da dama sannan suka saci shanu da sauran dabbobin ƴan ƙauyen.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, a wata sanarwa da ya fitar, Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, ya ce ƴanbindigar sun sace mutum biyu ma sannan suka kashe mutum ɗaya a ranar Lahadi, a Maraban Kajuru.
