Home Labarai Ƴanbindiga sun kashe mutum 13 a Katsina

Ƴanbindiga sun kashe mutum 13 a Katsina

34
0

Ƴanbindiga sun kai hari a karamar hukumar Sabuwa, jihar Katsina, inda suka kashe mutum 13 tare da raunata wasu.

Wani mazaunin garin ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa harin ramuwar gayya ne bayan kwace shanu da ƴanbindigar suka yi daga hannun wasu matasa da ke dibar yashi da su amma matasan suka kwato shanun.

“Bayan kwace shanun daga hannun matasan, sai samarin suka gayyato abokansu suka kwato su daga hannun yanbindigar.

“Hakan ne ya sa ƴanbindigar suka gayyato abokansu sama da 100 suka rika harbin duk wanda suka gani a kauyen,” inji shi.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne da yammacin ranar Talata.

An binne mutum biyu a ranar Talatar, sai kuma mutum 11 da aka yi wa sallah a masallacin juma’ar garin ranar Laraba.

Saidai rundunar ƴansandan jihar Katsina ta musanta kai harin tana mai cewa lamarin ya auku ne a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Majiyar DCL Hausa ta kuma samu rahoton cewa ƴanbindiga sun kashe wani mutum mai suna Haruna Tsaunin Batsi tare da raunata wasu biyu a Tsaunin Batsi da ke yankin Sayau a karamar hukumar ta Sabuwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply