Home Labarai Ƴanbindiga sun kashe mutum 6 a Kaduna

Ƴanbindiga sun kashe mutum 6 a Kaduna

51
0

Mutun shida sun mutu, wasu da dama kuma sun samu rauni sakamakon harin ƴanbindiga a kananan hukumomin Chikun da Giwa a jihar Kaduna ranar Asabar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya ce maharan sun kashe mutum biyu a yankin Maskoro da ke Kakau da wasu biyu a Akunakwo da ke Gwagwada, duk a karamar hukumar Chikun.

Sai kuma wasu mutum biyu da aka kashe a tsakanin Hayin Inji da Kidandan da ke Karamar Hukumar Giwa.

Kwamishinan ya kuma tabbatar da mutuwar mutum daya da jikkatar wasu mutum tara a harin ranar Juma’a a yankin yan rake da ke Galadimawa a karamar hukumar Giwa inda ƴanbindiga suka rika harbi kan mai uwa da wabi suka kuma jefa abin fashewa.

Gwamna Nasir el-Rufai ya jajanta faruwar wadannan al’amuran yana kuma addu’ar samun rahama ga mamatan tare da jajanta wa iyalansu.

Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su sake zage damtse domin dakile sake aukuwar hakan a fadin jihar, inji Kwamishinan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply