Home Labarai Ƴanbindiga sun kashe shi saboda ya ki sayen shanun sata

Ƴanbindiga sun kashe shi saboda ya ki sayen shanun sata

94
0

Wasu ƴanbindiga sun kai hari Sabon Garin Tabkin Kazai da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara inda suka kashe wani sanannen dillalin shanu saboda kin amincewarsa na siyan shanun da aka sato.

Mazauna yankin sun shaida wa majiyar DCL Hausa cewa, maharan da suka yi wa garin shigar ba zata, kai tsaye suka nufi wurin dillalin shanun mai suna Audu Mai Sayen Shanu, wanda aka fi sani da Audu na Ƴar Yaye kuma suka harbe shi nan take suka gudu.

Sun ce, “Audu ya shahara sosai a gabashin karamar hukumar ta Tsafe kuma a hakikanin gaskiya baya da tsara wajen sayan shanu.”

“Sau da yawa sun saba kawo masa shanun sata amma sai ya ki amincewa tare da yin watsi da bukatarsu ta neman kulla wata alaka ta kasuwanci da su.”

Ƴan garin sun kuma ce ya rika shaida masu cewa tun da dade wa ya daina harkar shanu bayan ya fahimci cewa shanun sata sun mamaye kasuwanni da dama a wannan shekara.

“Bayan da suka kashe shi sun kama gabansu ba tare da karbar ko sule a hannunsa ba kuma galibin mazauna garin ba su da masaniyar an kashe shi saboda shi kadai suka kawo wa takakka,” a cewar mazaunan.

Ya zuwa tattara wannan rahoto, babu wani bayani da ya fito daga rundunar ƴansanda ta jihar Zamfara dangane da lamarin kuma duk wani kokari da Aminiya ta yi na tuntubar mai magana da yawun ƴansanda na jihar, SP Muhammad Shehu, amma abin ya ci tura.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply