Home Labarai Ƴanbindiga sun sace dagaci da wasu mutum 9 a Katsina

Ƴanbindiga sun sace dagaci da wasu mutum 9 a Katsina

174
0

Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa ƴanbindiga sun sace mai Garin Gamji a ƙaramar hukumar Sabua Malam Falalu Galadima tare da wasu mutane tara.

Da yake tabbatar da batun, kakakin rundunar ƴansandan jihar SP Gambo Isah ya ce tuni aka baza jami’an tsaro cikin daji domin ceto mutanen cikin ƙoshin lafiya.

Saidai kuma wani mazaunin ƙauyen da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust mutum 13 ƴanbindigar da suka dira ƙauyen da misalin ƙarfe 1:30am na daren ranar Laraba suka sace.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply