Da sanyin safiyar ranar Talatar nan ne ƴanbindiga suka dira ƙaramar hukumar Matazu a jihar Katsina tare da yin awon gaba da surikar ɗan kasuwar nan Alhaji Ɗahiru Bara’u Mangal, Hajiya Rabi.
Wata majiya daga iyalan gidan, ta ce ƴanbindigar sun iso garin ne da misalin ƙarfe ɗayan dare kuma kai tsaye suka tunkari gidan Hajiya Rabi tare sa yin awon gaba da ita.
Majiyar ta ce kafin nan, sai da ƴanbindigar suka sace surikin ɗanta wani Buhari Muntari a cikin garin Katsina.
Mijin Hajiyar da aka sace Alhaji Muntari Masanawa ya tabbatarwa ƴanjarida a Katsina faruwar lamarin.
