Home Labarai Ƴanbindiga sun tilasta manoma guduwa ƙasar Nijar a Sokoto

Ƴanbindiga sun tilasta manoma guduwa ƙasar Nijar a Sokoto

86
0

Mazauna yankin ƙananan hukumomin Gudu da Tangaza na jihar Sokoto sun koka kan yadda ƴan bindiga suka addabesu wanda dole suke guduwa zuwa kasar Nijar don neman mafaka.

Sun bayyana cewa ƴanbindigar sukan shiga garuruwan nasu kullum su kashe su sannan su sace masu kudi a cikinsu don karbar kudin fansa.

Daya daga cikin ƴan kauyen Kurdula da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida cewa da yawa daga cikin su basa iya kwana gidajensu sai dai washe gari su dawo daga mabuyarsu a kasar Nijar.

Kwamishinan tsaro na Jihar Garba Moi Isa ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ci gaba da samun nasara akan ƴanta’adda da suka addabi jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply