Home Labarai Ƴanbindiga sun yi faɗa tsakaninsu a Katsina

Ƴanbindiga sun yi faɗa tsakaninsu a Katsina

59
0

Wasu gungun ƴanbindiga biyu sun yi faɗa tsakaninsu a ƙauyen Illela da ke ƙaramar hukumar Safana jihar Katsina, inda aka kashe da daman su, wasu kuma suka jikkata.

Faɗan ya faru ne ranar Alhamis, tsakanin ɓangaren Mani Sarki da Ɗanƙarami wanda ke samun goyon bayan ɓangaren Abu Rada.

Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa daga cikin abun da ya janyo faɗan shi ne; ƴanbindigar sun ware Sarki daga cikinsu ne, bayan ya tuba tare da rungumar shirin gwamnati na yin afuwa garesu.

Hakan ya sanya shi dawowa Illela domin fara sabuwar rayuwa amma wasu daga cikin yaransa suka ƙi bin sa.

Wata rana wasu ƴanbindiga ƙarƙashin jagorancin Ɗanɗa daga tawagar Ɗanƙarami suka kai hari Illela, amma ɗaya tawagar ta tare su, wanda hakan ya sanya su guduwa suka bar makamansu, ciki har da bindigar harbo jirgi da ta zama ganima, saidai kuma waɗanda suka kawo harin ba su haƙura ba.

Sannan kuma ƙanin Mani Sarki ya taɓa yin garkuwa da matar ɗaya daga cikin mutanen Ɗangwate sai da aka biya shi ₦500,000 sannan ya sake ta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply