Home Labarai Ƴansanda sun kama mutum 7 da zargin aikata tsafi da fashi a...

Ƴansanda sun kama mutum 7 da zargin aikata tsafi da fashi a Abuja

38
0

Rundunar ‘yansanda a babban birnin tarayya (FCT) ta ce ta cafke mutum bakwai da ake zargi da ayyukan kungiyar asiri, fashi da makami da kuma satar mutane a yankunan Kabusa, Bwari, Kwali, Gwagwalada da Abaji.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ASP Mariam Yusuf, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Mariam ta ce an kama wadanda ake zargin ne a yayin da rundunar ta gudanar da wani samame na leken asiri daban-daban a watan Janairun nan da ke karewa.

Ta kara da cewa biyu daga cikin wadanda aka kaman ana zarginsu ne da yin fashi da makami da kuma yunkurin aikata garkuwa da wani a hanyar Abaji.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply