Home Labarai Ƴanta’adda sun kashe mutane 21 sun sace 40 a jihar Neja

Ƴanta’adda sun kashe mutane 21 sun sace 40 a jihar Neja

42
0

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ƴanta’adda sun kashe mutane 21 gami da sace wasu 40 a wani sabon hari da suka kai a wasu yankuna na karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Wani da ya shaida faruwar lamarin, ya bayyana cewa ƴanbindigar da yawansu ya kai 300 sun farmaki ƙauyukan Kurege, Sabon Gida, Sararai da Rafin Kanya a ranar Litinin, inda suka yi ta harbi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa daga bisani kuma suka tafi da wasu.

Sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai tabbatar da adadin mutanen da lamarin ya shafa ba.

Matane ya shaida cewa gwamnati na iya bakin kokarinta don ganin ta shawo kan matsalar tsaro a fadin jihar baki daya.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar yandandan jihar ASP Wasi’u Abiodun ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply