Wasu majiyoyin tsaro sun ce sojoji 10 ne aka kashe a tsakiyar kasar Mali mai fama da rikici, bayan ‘yan tada kayar baya sun kai hari a sansanin sojojin a ranar Laraba.
Wani daga cikin majiyoyin ya ce wasu ne dauke da muggan makamai suka kai hari a sansanin sojojin a yankin Boni da ke tsakanin Douentza da Hombori a yankin Mopti.
Majiyar da ani jami’in tsaro da jami’in karamar hukuma a yankin sun tabbatar da cewa harin, ya raunata sojoji da dama.
Wani jirgi mai saukar angulu mallakin rundunar wanzar da zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya ta maida gawarwaki 10 a filin jirgin Sevare da ke kusa da garin na Mopti.
Kungiyar Tadayt mai alaka da Al-Qaeda ce dai ta dauki nauyin kai harin.
