Home Kasashen Ketare Ɓatanci ga musulunci: Ana zanga-zangar ƙyamar Faransa a Indonesia

Ɓatanci ga musulunci: Ana zanga-zangar ƙyamar Faransa a Indonesia

94
0

Kimanin mutane 400 ne suka taru a ofishin jakadancin Faransa da ke babban birnin Indonesia domin nuna ɓacin ran su ga zane-zanen ɓatanci da ake yi wa Annabi Muhammad S A W a ƙasar Faransa.

Masu zanga-zangar sun riƙa ɗaga fastoci tare da kiran shugaban Faransa Emmanuel Macron a matsayin maƙiyin musulunci.

Biyo bayan wasu hare-hare kan Faransa tun daga shekarar 2015, wanda ya yi silar mutuwar sama da mutane 250, a baya bayan nan ne Macron ya shata wani tsarin ɗaukar matakin kawo ƙarshen ƴan gwagwarmayar musulunci.

Saidai wasu musulmi na ganin matakan nasa sun yi tsauri yayin da wasu ke ganin yana munana kalamansa a yayin da yake zantuka kan musulunci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply