Home Labarai Ɓoyayyen lamari a rikicin Amotekun da Fulani makiyaya a Oyo

Ɓoyayyen lamari a rikicin Amotekun da Fulani makiyaya a Oyo

96
0

Harin da aka kai rugar Fulani da ke kauyen Igangan a ƙaramar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar Oyo ransr Juma’a, bayan ƙarewar wa’adin da wani shugaban matasan yankin Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho ya ba Fulanin, ya ƙara tsananta fargabar da ta mamaye yankin.

Sati ɗaya ne dai, bayan wani rikici tsakanin jami’an Amotekun na jihar Oyo da makiyayan a rugar Okebi, da ke Ibarapa ta Arewa, Sunday Igboho ya dira Igangan musamman a Rugar Sarkin Fulani Alhaji Abdulƙadir Salihu tare da umurtarsu, su bar masu ƙasarsu.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙurar faɗan Fulanin da Amotekun da ta yi silar mutuwar Fulani uku bata lafa ba, wanda hakan ya ƙara fargaba a zukatan makiyaya da manoma a yankin.

Daily Trust ta rawaito cewa a ranar Asabar ne jami’an Amotekun suka dira ƙauyen Okebi, a wani yunƙuri da suka kira faɗa tsakanin hukumar da Fulani da ake zargin masu satar mutane ne da suka addabi yankin.

Saidai kuma Fulani makiyayan, waɗanda da yawa sun rayu a yankin shekaru da dama sun ƙaryata wannan zargi da cewa an shigar wa wasu faɗa ne.

A kan wannan musayar zance ne dai rundunar ƴansandan jihar ta fara binciken rikicin da ya kai har da Gwamna Seyi Makinde ya tura tawaga ƙarƙashin jagorancin mai taimaka masa kan harkokin tsaro domin tantance ainihin abun da ya faru.

Kwamandan rundunar Amotekun na jihar Oyo Kanal Olayinka Olayanju mai ritaya, ya ce ba wani faɗa da ya auku tsakanin jami’ansa da Fulani, yana mai shaidawa ƴanjarida a Ibadan cewa rundunar ta ƙaddamar da aiki ne a ƙananan hukumomi huɗu, amma wasu ƴanbindiga suka hari jami’an a dajin Aiyete, inda har aka kashe uku daga cikin ƴanbindigar.

A cewarsa, aikin sintirin ya samu cikakken goyon bayan Fulanin yankin domin akwai wasu ƴan ƙungiyar Miyetti Allah ma a ciki.

Saidai kuma lokacin da majiya DCL Hausa ta ziyarci Rugar Okebi, wadda ke da nisan kilo mita biyu da garin Aiyete, Fulanin sun ce waɗanda Amotekun suka ce sun kashe ba ƴanbindiga bane, face makiyaya da suka rayu tsawon shekaru a yankin ba tare da an taɓa samunsu da wani laifi ba.

Waɗanda aka kashe sun hada da Alhaji Usman Okebi, wanda shi ne mataimakin Sarkin Fulanin jihar Oyo, sai Abdullahi Usman bafulatanin manomi da kuma wani Saidu Usman.

Mazauna Rugar, waɗanda ke makokin kisan ƴan uwan nasu na ranar Asabar, sun ce alaƙanta mutanen da ƴanbindiga abu ne da zai yi wa Fulani baƙin fenti.

Wasu daga cikin Yarbawan yankin da aka tambaya ko suna da masaniyar akwai maɓoyar ƴanbindiga a yankin, sun ce abu ne da zai iya yiwuwa, saidai ba su da wata hujja a kai.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply