Home Labarai Ɗansanda ya yi wa ɗaliba fyaɗe

Ɗansanda ya yi wa ɗaliba fyaɗe

137
0

An kama wani Jami’in ƴansanda da yake a caji ofis na Agbado a birnin Ikko, Adelakun Amubieya da laifin yi wa wata yarinya fyade a yankin Ipaja.

An rawaito cewa yarinyar ƴar shekara 18 suna zaune a gida daya da jami’in ƴansandan, inda ɗansandan da matarsa suka alkawarta wa yarinyar za su koya mata hanyar samun kudi ta hanyar amfani da wayar salularta.

Yarinyar ta shiga wurin Amubieye ta iskeshi shi kadai cikin gidan, daga nan ya jata cikin dakinshi inda ya yi mata fyade.

Bayan aukuwar lamarin ne mahaifin yarinyar ya kai ta asibiti don ba ta taimakon gaggawa wanda daga bisani ya kira Jami’in ta waya ya shaida masa halin da ake ciki shi kuma nan take ya musa zargin da ake masa.

Hakan tasa ya kai kararsa a ofishin ƴansandan, wanda a ka yi ta neman sa ba a sameshi ba har zuwa lokacin da aka samu damar kamashi a yammacin jiya Alhamis.

Da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na ƴansandan jihar, Muyiwa Adejobi ya ce zai sanar da halin da ake ciki da zarar sun kammala bincike kan lamarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply