Home Labarai Ɗaurin wata 6 ga wanda ya yi ɓatanci ga gwamnan Jigawa

Ɗaurin wata 6 ga wanda ya yi ɓatanci ga gwamnan Jigawa

74
0

Kotun Majistire dake Dutsen jihar Jigawa ta yanke hukuncin daurin wata 6 ga Sabi’u Chamo ko kuma tarar kudi ₦200,000, tare da bulala 20 saboda batancin da ya yi wa gwamnan jihar Muhammad Abubakar.

Alƙalin da ta yanke hukuncin Batula Dauda ta ce wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya yi batanci ga gwamnan.

A wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta ma’aikatar shari’a ta Jigawa Zainab Santali ta fitar a jiya, ta ce wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply