Home Kasashen Ketare Babu wanda ya isa ya ja dani – Donald Trump

Babu wanda ya isa ya ja dani – Donald Trump

122
0

Shugaban Amirka Donald Trump ya ya yi wata hira da jaridar kasar ta Washington Exerminer inda ya bayyana mata bayaninsa na shirin kalunbalantar sakamakon zaben kasar da aka gudanar ranar 3 ga Nuwamban nan.

Trump ya yi ikirarin cewa zai samu karin kuri’u daga jihohin da ka iya sauya sakamakon zaben kasar.

Ya ce jami’an zabe a jihohin Michigan, Pennsylvania sun ki ba wakilan shi damar su san kan yadda tsarin gudanar da zaben ya ke wakana, ya kuma kafe kan kin amincewa da sakamakon jihar Arizona.

Trump ya ce muddin idan aka sake yin bitar kuri’u to tabbas shi ne zai yi nasara.

Cikin hirar ta su shugaba Trump yayi wani kakkausan lafazi inda yace ” Ni ba a ja dani, duk wanda ya ja dani bazai ji dadi ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply