Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Farashin siminti ya sauko

Farashin siminti ya sauko

244
0

Farashin siminti ya sauko da kusan kaso 25% a birnin Enugu kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya rawaito.

A binciken da ya gudana a wasu kasuwanni, ya nuna cewa ana sayar da buhun siminti mai nauyin (50kg) Naira 2,800 zuwa 3,000 maimakon 3,800 a baya.

Pius Eze, wani dilan katako, yace farashin simintin ya sauko ne bayan samun wadatuwarsa a ‘yan kwanakin nan.

Innocent Uwakwe, wani dan kwangila, yace hawa da saukar da siminti ke yi ne ya sa gidaje ke tsada a yankuna.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply