Home Labarai Mun inganta hanyoyin ba da takardar mallaka ta “C of O” –...

Mun inganta hanyoyin ba da takardar mallaka ta “C of O” – Nadada

325
0

Kwamishinan kasa da safiyo na jihar Katsina Alhaji Usman Nadada yace gwamnatin Masari ta bullo da sabbin dabarun ba da takardar mallaka ta “Certificate of Occupancy” cikin kankanin lokaci a jihar.

Usman Nadada na magana ne a lokacin da ya ke ganawa da DCL Hausa a ofishinsa, inda ya ce har tsarin biranen jihar Katsina ma zai kara inganta ba da jimawa ba.

Yace gwamnatin ta samar da kayan aiki na zamani da ake amfani da su irin su kwanfita, domin a samu zarafin gudanar aiki a kankanin lokaci.

Kwamishinan yace ya zuwa yanzu ba a daukar dogon lokaci wajen samar da takardar, sabanin shekarun baya da ke cin dogon lokaci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply