Abdullahi Garba Jani
Sashen kula da albarkatun man fetur na Nijeriya ya ja kunnen mutane da su guji amsa waya a lokacin da suka je shan mai a gidajen mai.
Daraktan aikace-aikace na sashen a jihar Osun Mr Ademola Makinde ya ce wannan jan kunne ya zamo wajibi don dakile yawaitar tashin gobara.
Mr Makinde ya roki masu motoci da su rika kashe motocin kafin a zuba musu mai duk lokacin da suka ziyarci wuraren shan mai.

Sai ya karkata wajen ‘yankasuwar mai, ya ja kunnensu da su sabunta lasisinsu matukar dai wa’adinsa ya kare.
Mr. Makinde ya kuma ja kunnensu da su guji sayar da man kan farashin da ba na gwamnati ba.
Ya kuma ba mutabne shawara da a kodayaushe su rika bincikar murhunsu na zamani (gas cylinder) don gudun kada ya rika diga ba a sani ba da zai yi sanadiyyar tashin gobara.
