Home Labarai Yara sama da milyan daya ba su da takardar haihuwa a Legas

Yara sama da milyan daya ba su da takardar haihuwa a Legas

67
0

Abdullahi Garba Jani

 

Wata kididdiga daga wani tsarin tattara bayanan haihuwa na duniya “rapidSMS” ya fitar ta nuna cewa akwai yara ‘yan kasa da shekaru 5 a jihar Legas kimanin 1,436,986 da ba a yi musu rajistar shaidar haihuwa ba.

Kan haka ne, hukumar kidaya ta kasa ta wajabta wa gwamnatin jihar Legas cewa sai ta yi wa yara milyan daya rajistar haihuwa kafin wannan shekarar ta kare.

A ya yin wani taron bita na kwanaki biyu, jami’a daga asusun -UNICEF- Mrs Sharon Oladiji ta yi nuni da cewa karamar hukumar Epe a jihar ta Legas ta samu koma baya sosai wajen kin yin rajistar haihiwar yaran, inda take da yara 28,817, sai karamar hukumar Lagos Island mai yara 28,579 da kuma karamar hukumar Ibeju-Lekki mai yara 18,346 da ba a yi wa rajistar ba.

Mrs Sharon ta ce rajistar haihuwa ce matakin farko da za a gane zuri’ar yaro, amma jihar Legas ta gaza cimma wannan matakin na yin rajistar yara.

Ta yi takaicin cewa sama da yara milyan daya da rabi na fuskantar barazanar tauyewar hakki ta fuskar rajistar haihuwa.

Dokar Nijeriya ta 69 ta shekarar 1992 ta jaddada cewa a yi wa kowane yaro da aka haifa rajistar haihuwa kyauta cikin kwanaki 60 da aka haife shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply