Home Coronavirus Almajirai 16 daga cikin wadanda aka mayar jihar Jigawa na dauke da...

Almajirai 16 daga cikin wadanda aka mayar jihar Jigawa na dauke da Covid-19

200
0

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta karbi sakamakon gwajin almajirai 45 da aka yi masu kan cutar coronavirus.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abba Zakari ya bayyana haka ga ‘yan jarida a ranar Alhamis a sansanin horas da matasa masu yi wa kasa hidima, inda aka killace almajiran.

Ya bayyana cewa sakamakon gwajin almajirai 16 ya nuna suna dauke da cutar yayin da sauran aka tabbatar ba su dauke da ita.

Zakari ya yi bayanin cewa yaran 45 na daga cikin Almajirai 607 da aka debi jininsu, bayan an dawo da su daga jihar Kano.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply