Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ayyana ranar 16 ga watan Satumba a matsayin ranar katin ɗan ƙasa, tare da nuna ko wane ɗan ƙasar ya mallaki katin shaida.
Ministan sadarwa Dr Isah Ali Pantami ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman ta fitar ranar Talata, a Abuja.
Pantami ya tunatar da ƴan ƙasar muhimmancin mallakar katin shaidar, yana mai cewa ma’aikatarsa ta samar da tsari mai kyau da zai bada damar samun katunan shaida ta intanet.
