DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeBinciken Gaskiya (Fact Check)Da gaske ne za a ɗaure ɗaliban da suka gaza biyan bashin...

Da gaske ne za a ɗaure ɗaliban da suka gaza biyan bashin NELFUND?

Asusun bayar da lamunin ilimi na Nijeriya (NELFUND) ya yi watsi da wani labari da ke yawo a kafofin sada zumunta da ke iƙirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da hukuncin ɗaurin rai-da-rai ga duk ɗalibin da ya gaza biyan bashin karatunsa bayan ya kammala karatu, inda ya bayyana labarin a matsayin ƙanzon ƙurege.

Jaridar Punch ta bayyana cewa asusun na NELFUND ya wallafa a shafinsa na dandalin X a ranar Lahadi wani hoto da aka ƙirƙira na shafin farko na jaridar The Daily Tribune mai ɗauke da kwanan watan Alhamis, 27 ga watan Mayun 2027, inda asusun ya buga tambarin “FAKE” wato ƙarya a kansa.

Asusun ya jaddada cewa wannan iƙirari ba shi da tushe ballantana makama, yana mai tunatarwa cewa an kafa asusun ne a ƙarƙashin dokar ba da lamunin ɗalibai ta shekarar 2024 domin bayar da bashin karatu ba tare da ruwa ba ga ɗaliban manyan makarantun gwamnati.

A ƙarƙashin dokar da ta kafa hukumar, biyan bashin na fara aiki ne bayan shekaru biyu da kammala aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC), kuma idan ɗalibin ya sami aikin yi ne kawai.

Dokar ta tanadi cewa za a riƙa cire kaso 10 ne kawai daga albashin mai cin gajiyar bashin a kowane wata ta hannun mai ɗaukarsa aiki, yayin da masu sana’ar dogaro da kai kuma ake buƙatar su riƙa biyan makamancin wannan kaso daga abin da suke samu.

‘Ga waɗanda kuma ba su sami aikin yi ba bayan cikar shekaru biyun, suna da damar neman ƙarin lokaci ta hanyar gabatar da rantsuwar kotu (affidavit)’, in ji NELFUND

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata