Home Labarai 2021: An kafa dokar hana fita a Lagos

2021: An kafa dokar hana fita a Lagos

124
0

Kwamishinan ‘yansanda na jihar Lagos Hakeem Odumosu ya ba jami’an rundunar umarnin tabbatar bin dukkan ka’idojin kariya daga kamuwa da cutar Covid-19 da kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar ya gindaya.

Odumosu ya umarci jami’an rundunar su saka dokar hana fita a fadin jihar daga karfe 12 na dare zuwa karfe 4 na asuba.

Bayanin hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Alhamis, a daidai lokacin dai coci-coci ke kokarin gudanar da ayyukan ibada a daren 31 ga watan Disambar nan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply