Wata kungiya mai suna Nasiriyya for Nigeria a ranar Talata ta gudanar da wani taro a Kaduna, inda ta bukaci jama’a su yi AZUMI ko su biya kudin zuwa UMRAH domin Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai ya tsaya takara kuma ya yi nasarar cin zaben shugaban kasa na shekarar 2023 idan Allah Ya Kai mu.
Gidan rediyon jihar Kaduna a cikin shirin siyasa mai suna “Bakin Zaren” wanda a kasa a daren Larabar nan ya ruwaito shugabannin wadannan kungiya suna cewa samun Elrufai a matsayin shugaban Nijeriya zai ba da dama kasashen nahiyar Afirka su ci gajiyar basirarsa da hangen nesa ba ma Nijeriya kadai ba.
Shin ya kuke kallon wannan yekuwa ta su? Za ku iya AZUMI ko zuwa UMRAH don wani shugaba na siyasa ya lashe zabe?
