Home Labarai 2023: Za mu sauya tsarin amfani da ‘Card Reader’ – INEC

2023: Za mu sauya tsarin amfani da ‘Card Reader’ – INEC

45
0

Hukumar zaben Nijeriya INEC ta ce ta fara bitar tsarin fasahar da take amfani da shi a zabuka da manufar shigo da sabbin hanyoyin inganta zaben kasar kafin nan da shekara ta 2023.

Daraktan sashen wayar da kan masu zabe da yada labarai na INEC Nick Dazang ya bayyana haka a ranar Talata, lokacin wani taron karawa juna sani da sashen ya shirya domin bitar littafin wayar da kan masu zaben, wanda ya gudana a Birnin Keffi na jihar Nasarawa.

Da yake magana da ‘yan jarida kan muhimmancin taron wanda hukumar ta shirya hadin guiwa da Gidauniyar ‘Westminster Foundation for Democracy’, Dazang ya ce INEC ta fara amfani da kwamfuta lokacin zabe tun a shekarar 2004, kuma tana ci gaba da inganta tsarin don ya dace da zamani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply