
Al’amura sun soma komawa daidai a unguwar Tudun Yola da ke Kano.
Rikicin jagoranci ya tilasta rashin yin sallar Jumu’a a Masallacin Darul Hadith na marigayi Dr. Ahmad Ibrahim BUK.
Tarzoma ta kaure a Masallacin ne lokacin da sabon liman zai hau Mumbari don soma huɗu ba, inda wasu fusatattu suka janyo rigarsa ta baya don nuna ƙin amincewa da shi, lamarin da ya kawo rikici.
Tuni aka rufe masallacin tare da baza jami’an tsaro a kofa da kewayensa.
Yanzu haka dai tuni ɓangarorin biyu suka nufi shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai domin sasantawa kamar yadda Freedom Radio Kano ta rawaito.
Subhannallah! Allah ya gafartawa mallam, amin.
Don Allah muji tsoron Allah mu cire son zuciyar mu wajen son JAGORANCIN al’umma musamman irin wannan na LIMANCI. Muyi hattara domin duniya tana kallon Mallammai sune ke daidaita kan al’umma ba su rabata ba. Allah ya sa mu gane kuma mufi karfin zuciyar mu, amin.