Boka ya dirka wa mai neman magani ciki a Kano
Hukumar Hisbah a karamar hukumar Dawakin Kudu a jihar Kano ta kama wani boka mai suna Muhammad Mansur bisa zargin ya dirka wa wata mata da ke zuwa wajensa neman magani ciki.
An kama bokan da ke zaune a kauyen Kode ne bayan da matar da ta kai kararsa ga hukumar Hisbah, inda take neman a yi mata adalci game da cikin da take dauke da shi dan wata bakwai.
Rahotanni daga kauyen kamar yadda Daily Trust ta sanar, sun ce dama an san mutumin da yaudarar mata ciki hada matan aure, inda ya ke ce musu idan suka aminta ya yi lalata da su, zai ba su wasu layu da za su sa mazajensu su gaza kara aure, kuma matan za su mallake mazajensu.
Matar ta ce ta je neman magani ne a wurin bokan, amma ya ce mata maganin ba zai yi aiki ba har sai ya yi lalata da ita.
Ta sanar da Hisbah cewa mutumin ya sha kokarin lalata da ita tun lokacin da suka fara zuwa da mamarta, amma dai bai yi nasara ba har sai ranar da ta je ita kadai ba tare mamarta ba in
Boka ya dirka wa mai neman magani ciki a Kano
Hukumar Hisbah a karamar hukumar Dawakin Kudu a jihar Kano ta kama wani boka mai suna Muhammad Mansur bisa zargin ya dirka wa wata mata da ke zuwa wajensa neman magani ciki.
An kama bokan da ke zaune a kauyen Kode ne bayan da matar da ta kai kararsa ga hukumar Hisbah, inda take neman a yi mata adalci game da cikin da take dauke da shi dan wata bakwai.
Rahotanni daga kauyen kamar yadda Daily Trust ta sanar, sun ce dama an san mutumin da yaudarar mata ciki hada matan aure, inda ya ke ce musu idan suka aminta ya yi lalata da su, zai ba su wasu layu da za su sa mazajensu su gaza kara aure, kuma matan za su mallake mazajensu.
Matar ta ce ta je neman magani ne a wurin bokan, amma ya ce mata maganin ba zai yi aiki ba har sai ya yi lalata da ita.
Ta sanar da Hisbah cewa mutumin ya sha kokarin lalata da ita tun lokacin da suka fara zuwa da mamarta, amma dai bai yi nasara ba har sai ranar da ta je ita kadai ba tare mamarta ba.
Allah y kyauta